KAI TSAYE DAGA MINISTRY OF JUSTICE POTISKUM.
MUZAHARAR FREE ZAKZAKY TA DAGA DA SUNAN ALLAH. Yau ma kamar Jiya Yan uwa musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na garin Potiskum Sun sake Bayyana Gaban Babban Kotu Dake Tsakiyar Garin Potiskum domin sake Jaddada musu irin zalunci da akewa Sheikh Ibrahim Zakzaky da sunan Shari'a. Idan ba'a manta ba tun a Shekarar 2016 Wata Babbar kotu a Abuja karkashin Gibrel Kolawale ta yanke hukunci Asaki Malam amma wannan Tsinanniyar Gwamnati tayi burus da maganar. Daga karshe an sake tunatar da Yan uwa a cigaba da yin Addu'oi da Kuma kasancewa cikin Shirin sake Fitowa Muzaharar Aduk Lokacin da aka bukaci Yan uwa da su fito. Anfara Lapiya Kuma Ankammala Lapiya. 🖊️🖊️🖊️AMS. 09/03/2021.
Comments
Post a Comment