GOBE ZA A CIGABA DA HARAMTACCIYAR SHARI'AR DA AKE WA SHAIKH ZAKZAKY DA MATARSA A KADUNA
GOBE ZA A CIGABA DA HARAMTACCIYAR SHARI'AR DA AKE WA SHAIKH ZAKZAKY DA MATARSA A KADUNA
Idan ba ku manta ba dama kotun ta dage cigaba da sauraron shaidun da Lauyoyin gwamnati suke gabatarwa ne zuwa ranar 8 da 9 ga watan Maris 2021.
Tun a ranar Laraba da Alhamis 18-19/11/2020 ne Lauyoyin gwamnatin jihar Kaduna suka fara gabatar da shedunsu a kokarinsu na gamsar da kotu kan hauka da shirme da suke wa Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah, inda a ranar Laraba 18 ga Nuwambar suka gabatar da shedu biyu da suka hada da Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, wanda yake tsohon kakakin rundunar sojan Nijeriya ne a lokacin kisan-kiyashin Zariya har zuwa ritayarsa. Ya tabbatar da cewa yana tare da tawagar Buratai a yayin kisan-kiyashin Zariya, sannan kuma bai yi magana da Shaikh Zakzaky ba a tsawon wannan lokacin.
Shaidan lauyoyin gwamnati na biyu da suka gabatar shine Kanar Babayo Muhammad wanda, wanda yace a yanzu haka shine kwamandan 25 Birget a Damboa jihar Borno, kuma a lokacin da aka yi kisan-kiyashin Zariya shine kwamandan sector 2 na Operation Yaki a jihar Kaduna, kuma shine aka tura shi tare da sojoji 40 suka yi ‘operation’ a Darur Rahma a kokarinsu na kamo Shaikh Zakzaky.
Babayo yace lokacin da aka tura su Dembo (Darur-Rahma) tare da sojoji 40, suna tsaye sai wani mutum da fararen kaya ya tunkaro su rike da wuka a hannunsa yana Allahu Akbar! Sai shi ya ja da baya ya shiga wani masallaci a wajen, yana shiga sai wata mace da wasu maza suka zo suka rike shi suka kwace bindigarsa mai dauke da harsasai 60 suka caka masa wuka suka bar shi a wajen sun dauka ya mutu.
Dukkansu shedun biyu bayan da suka ba da shedarsu, lauyan Shaikh Zakzaky, Femi Falana ya rika musu tambayoyin da a ka’ida sun sani, amma sai suke ba da amsa da basu sani ba ko sun manta.
Washegari Alhamis 19/11/2020 lauyoyin gwamnati suka gabatar da shedu mutum hudu. Shedun sun hada da: Alhaji Muhammadu Abba Girei, tsohon Daraktan Operation a Hedikwatar DSS da ke Abuja, wanda kuma shi aka far aba tsaron Shaikh Zakzaky bayan sojoji sun mika shi ga hannun DSS. Amma shima da ya gama ba da bayaninsa, duk tambayar da Falana ya masa sai yace bai sani ba ko ya manta, kamar yadda shedun da suka gabata suka yi.
Alhaji Muhammadu, wanda lokacin da aka basu tsaron Shaikh Zakzaky suna cikin halin rashin lafiya ne, har ma a karkashin kulawarsa ne aka aje Shaikh din a asibitin DSS tsawon watanni uku cur, amma sai yacewa kotu bai san ko Shaikh Zakzaky na rashin lafiya ba, kawai ka’idarsu ce ta DSS duk wanda suka kama suna aje shi ne a asibiti.
Shaidan gwamnati na hudu shine Muktar Gambo, wanda ya bayyana cewa shine mataimakin shugaban kungiyar matasan Gyallesu a Zariya, kuma shi Ahlussunnah ne (Bawahabiye), wanda yace kawai su basu son zaman Malam Zakzaky a Gyallesu. Bayan da ya gam aba da shaida Lauya Falana ya masa tambayoyi ya amsawa kotu kafin a sallame shi.
Shedan Gwamnati na biyar shine Shamsuddeen Aliyu Ahmad wanda yace shima mazaunin Gyallesu ne. Yace a shekarar 2013 yaran Malam sun sare shi a kai, aka je wajen yan sanda aka kai shi asibiti. Shima da Falana ya tambaye shi ko ya san wanda ya sare shi din? Yace bai san shi ba.
Sheda na shida shine Musa Isiyaku shi ma Ahlussunnah ne wanda yace yana zaune ne a gida mai lamba 21 a layin Sarkin Yaki a unguwar Gyallesu, wanda shima yace wani a cikin yaran Malam ya taba saran babansa Madakin Gyallesu da wuka a kafa, suka kai shi asibiti ya yi jinya, bayan wata hudu da saran ya mutu. Shima da Falana ya tambaye shi ko ya san wanda ya soki baban nasa da wukar? Yace ya san shi, sunansa Ruhana. Ko sun kai kara wajen hukuma a lokacin? Yace ba su kai ba. Ko ya san ranar da mahaifin nasa ya rasu? Yace bai sani ba.
Bayan gabatar da wadannan shedun ne aka dage shari’ar zuwa 25 da 26 ga Junairun 2021 don cigaba da sauraron shedun.
A ranar 25/1/2021, lauyoyin gwamnati sun cigaba da gabatar da shedunsu ne, inda suka kawo mutum hudu da suka hada da Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ACP Ibrahim Abdul, wanda yanzu shine kwamandan 47 PMS da ke Zaria, wanda yace shi ne aka damkawa wadanda sojoji suka kama bayan kisan-kiyashin Zariya.
Sai kuma wani tsohon soja kuma likita, mai suna Kanar Dakta Gideon Iko Ayuba mai ritaya, wanda yace shi ya duba gawar Soja Yakubu Dan Kaduna da ake zargin an kashe shi a Zariya, ya kuma bayyana cewa an kawo gawar sojan asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna ne a ranar 13/12/2015, amma sai a ranar 21/12/2015 aka kira shi don ya gwada gawar, kuma bincikensa ya nuna masa cewa gawar ta mutu akalla kwana daya kafin ranar da aka kawo ta asibitin.
Sauran shedun da suka gabatar sun hada da Ishaq Sani daga kauyen Gabari, wanda yace a shekarar 2014 ‘yan shi’a sun yi yunkurin kwace musu Masallaci. Da kuma sheda na gaba mai suna Musa Saminu daga unguwar Aska a cikin garin Zariya, wanda shi ma yace a shekarar 2014 lokacin yana dalibin jami’a almajiran Malam Zakzaky sun tsare shi a hanya saboda ya tsaya a kan titi lokacin da tawagar Malam ke wucewa inda suka masa barazanar za su kashe shi. Inda duk Lauyan Shaikh Zakzaky, Mr Falana SAN ya ce ba zai musu tambaya ba saboda abin da suke fada bai shafi shari’ar da ake yi ba.
Washe gari 26/1/2021 aka koma kotun, inda suka gabatar da sheda guda daya wanda yake kwamandan Kungiyar Izala ne kasa mai suna Alaramma Imam Mustapha Sitti, wanda yace shi mazaunin unguwar Gyallesu ne tun a shekarar 1977, ya kuma yi kokarin nuna cewa tun da Shaikh Zakzaky ya tare a unguwar a shekarar 1999 yake takura musu, kuma basu son zamansa. Sai dai da lauyan Shaikh din ya masa tambaya, Sitti bai boye cewa akwai gaba tsakanin kungiyarsa da Aqidar Shaikh Zakzaky ba.
Har ila yau a wannan ranar, lauyoyin Gwamnatin sun so su gabatar da sheda na biyu mai suna Hon. Muhammad Ali, tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Bawahabiye kuma tsohon jami’in tsaro na SSS, wanda ya so ya kunna wani faifan Bidiyon jawabin Shaikh Zakzaky na ranar tunawa da Shahidai a shekarar 2015 wanda suka yanko na ‘yan sakonni don ya gabatar a matsayin hujja, sai dai lauyoyin su Malam (H) din suka ce basu yarda ba, domin kuwa a jiya aka basu bidiyon, saboda haka suna bukatar lokaci don nazartansa da sanin me ya kunsa don su san yadda za su ba da kariya. Inda kuma kotun ta amince da wannan bukatar tasu.
Daga nan sai kotun ta sanya ranar 8 da 9 ga watan Maris din 2020 don cigaba da shari’ar. Don haka gobe Litini da Jibi Talata za a cigaba da wasan kwaikwayon.
Allah Ta'ala Ya jibinci al'amarin Shaikh Zakzaky, ya masa sakayya a kan azzalumai.
Comments
Post a Comment