YA ZA KA ZAMA SHAHIDI (III)
WANNAN BA ABUN DAMUWA BANE!
Dan mutum ba'a kashe shi a Tafarkin Allah ba ba shi ke nifin shikenan bai samu yardar Allah ba.Domin akan samu mutum ya qarar da rayuwar shi a Tafarkin Allah,amma sai ya rinqa damuwa saboda ya ga zai wafati a kan gado. Kwata-kwata wannan ba daidai bane; Domin Hadafin shine tsayuwa qem kan Tafarkin Har zuwa qarshen Rayuwa. Shi ne ma'anar faɗin Allah (T) cewa,"Daga cikin muminai akwai wasu mazaje sun gaskata abin da su kai wa Allah alqawari (Na tsayuwa a Tafarkin Allah har qarshen rayuwarsu) daga cikinsu akwai wanda ya cika alqawarinsa (Ya mutu ko yai shahada) daga cikinsu kuma akwai mai jira (ɗayan biyun ya same shi) kuma ba su canza ba canzawa", (Al-ahzaab,23).
Idan muka kalli wannan aya da kyau za mu fahimci cewa da wanda aka kashe a Tafarkin Allah, da wanda ya mutu a Tafarkin duk sun cika alqawari. Illa iyaka samun Shahada a Tafarkin zaɓi ne na Allah ga wanda ya so ya ba.
Jagoran gwagwarmayar Tabbatar da addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzakiy (H) na cewa a wannan gaɓar, ". .. Shi cika alqawari, ba sai kai Shahada ne ka cika alqawari ba, ainihin ko cikawa ya same ka kana tsaye qem ka cika alqawari... ", (Wani yanki na jawabinsa).
Sannan kuma bugu-da-qari baya ga cikawa a Tafarkin Allah wanda kuma itace babbar manufa, akwai wasu ayyuka da idan mutum ya tsayu da yinsu Allah zai kai shi ga wannan matsayin koda ya mutu a kan gadon shi.
A dakace ni
[4/5, 8:41 AM] Aɗɗalib Ahmad Harun: YA ZA KA ZAMA SHAHIDI (IV)
An samo Hadisi daga Manzon Allah (S) inda yace, "Wanda ya roqi Allah Shahada da gaskiya Allah zai kai shi maqaman Shahidan koda ya mutu a kan gadonsa". Sannan a wata ruwayar kuma yace,"Wanda ya nemi Shahada yana mai gaskiya (Kan roqon) Za'a bashi ita koda ba ta same shi ba,"(Durus min kaɗɗil-Imamil-Khumainiy, 62).
A nan in mu kai duba, za mu ga kyakkyawar Niyyar mutum ga Shahadar kan iya kai shi ga matsayin.
Har wala lau, an ruwaito cewa, duk wanda ke karanta Suratul-Kahfi duk daren Juma'a ba zai mutu ba sai yana Shahidi, (Mafatihul-Jinan, sashin ayyukan daren Juma'a). Sannan kuma Manzon Allah ya hore Imam Ali (A) da karanta ayatul-Kursiyyi duk bayan sallar farilla. Wanda shima a nan yace ba mai kiyaye yin haka sai Annabi ko Siddiqi ko Shahidi, (Mafatihu,888).
Sannan an ruwaito cewa, duk wanda ya karanta suratur-Rahman (Ar-rahmaan) Tare da cewa, 'La bi shai'in minal Aa'ika rabbi ukazzib' a bayan duk faɗin 'Fabi ayyi aalaa'i rabbi kumaatu kazzibaan'. To duk wanda ya karanta da wannan sigar da daddare sai ya mutu a daren to ya mutu Shahidi.Ha kazalika in yai haka da rana sai ya mutu a yinin nanma ya mutu a Shahidi, (Mafatihu, farkon-farkon littafin).
Wato in muka lura za mu fahimci cewa abin da ake buqata ga mutum shine aiki Tuquru! Sai dai kar a manta da Ikilasi a yayin aikatawan.
Wato abin da nake son nusarwa a 'yar maqalar nan shine, samun Shahada zaɓi ne na Allah Ta'ala ga wanda ya so sai ya ba, daga cikin wa'inda suka tsayu qem a Tafarkinsa. Sannan kuma dan mutum ya tsayu qem a Tafarkin ba'a kuma kashe shi ba ba shikenan bai cika alqawari ba, la la la! Madamar ya tsayu a Tafarkin har qarshen rayuwarsa to ya cika alqawari. Sannan kuma abin birgewa! Allah zai kai shi maqaman Shahidan in ya roqi Allah da kyakkyawar Niyya. Baya ga haka kuma ga wasu ayyuka da idan mutum ya tsayu da su suma za su riskar da shi ga wannan matsayin na Shahada.
Fatan Allah ya Tabbatar da digadiganmu kan Tafarkinsa har qarshen Rayuwarmu.
Allah muna qara kawo kukanmu kan halin da Jagoranmu da mai ɗakinsa suke ciki, ka qara kasancewa tare da su. Su kuma azzalumai kai musu abin da ya dace da su.
Comments
Post a Comment