MUHIMMAN AYYUKAN DA AKA FI SON YI A WATAN RAMADANA
TAREDA QA'EEM TV
Watan Ramadana wata ne da ke da ɗimbin ayyuka, kama daga salloli, zikrori, addu'o'i da sauransu. To, amma akwai muhimman ayyukan da ka fi son yi, sune;
🌷Karatun Al-ƙur'ani: Ya zo a cikin Huɗubar Manzon Allah (S) wacce yai gab da shiga watan Ramadana cewa, karanta aya ɗaya a watan Ramadana na daidai da sauke Al-ƙur'ani a wani watan na daban.
🌷Ciyarwa: Manzon Allah (S) ya ce, "Duk wanda ya ba mai azumi abin buɗa-baki to yana da lada irin nashi (Mai azumin) ba tare da an tauye wani abu daga ladar shi ba, kuma yana da ladar aikin da yai na alheri da ƙarfin wannan abincin (Da ya bashi)", (Mafitihul-Jinan).
🌷Istigifari: Ana son yawaita Istigifari, domin Allah na yawan karɓar tuba a watan. Kuma Hadisi ya zo daga Annabi (S) cewa, duk wanda watan Ramadana ya fita ba'a gafarta mai ba, to ba za'a gafarta mai ba sai dai in wani Ramadana ɗin ya zagayo!
🌷Addu'a: Duba da cewa watan wata ne na ƴantawa daga wuta, gafartawa, biyan buƙatu da sauransu, to ana buƙatar yawaita roƙon Allah gafara, fatahi da dai sauran buƙatun Alheri na Duniya da Lahira, musamman a lokacin sahur da buɗa-baki, sannan da ƙarshen dare!
Fatan Allah ya ƙarɓi Ibadunmu ya kuma biya mana buƙatun Alheri na Duniya da Lahira!
~Aɗɗalib Ahmad Harun
Comments
Post a Comment