WASIYYAR MANZON ALLAH (S) GA IMAM ALI (AS) GAME DA ZAMANTAKEWAR AURE KASHI NA (2)
TAREDA QA'EEM TV
*Manzon Allah (s) yace: Ya Ali (as) a satin farko na zuwan matarka gidanka ka hanata cin abubuwa guda hudu:*
*1-Ka hanata shan Nono.*
*2-Ka hanata shan abu mai tsami.*
*3-Ka hanata cin kuzbarat (كزبرة) [wani ganye ne da ake sakawa acikin abinci yakan bada wani dandano a abinci.]*
*4-Ka hanata cin Apple mai tsami.*
*Sai Imam Ali (as)Yace:Ya manzon Allah(s) saboda me zan hana mata ta cin wadannan abubuwa guda hudu??*
*sai manzon Allah (s) yace:Domin mahaifa tanayin sanyi kuma tana daina haihuwa saboda wayannan abubuwa guda hudu,kuma ka ajiye tabarma ajingine a jikin ginin gidanka it's tafi alkhairi akan matar da bata haihuwa.*
*sai Imam Ali(as)yace:ya manzon Allah (s) meye matslar abu mai tsami da har zaa hana amarya daga gareshi???*
*sai manzon Allah (s)yace:*
*1-Idan mace tayi haila bayan tasha wannan abu mai tsami bazata kara samin cikakken tsarki na hailarta ba har abada.*
*2-shi kuma ganyan kuzbarat (كزبرة) yana tayar da haila acikin mace, kuma yana daure haihuwarta.wato yazama tasha wahala kafin ta haihu.*
*3-shi kuma apple mai tsami yana yanke haila sai hailar tazama cuta ciwo acikin mace.*
*4-shi kuma Nono yanasa mahaifa tayi sanyi yazama ta daina haihuwa.*
*Insha Allah zamuci gaba.......*
*كتاب مكارم الاخلاق تأليف الشيخ الطبرسي (قدس)*
Comments
Post a Comment