YA ZA KA ZAMA SHAHIDI? (I)
~Aɗɗalib Ahmad Harun
Shahada na nufin a kashe mutum a tafarkin wani Hadafi maɗaukaki mai girma a cikin yardar Allah Ta'ala.
Kuma lallai ita shahada tana ɗaya daga cikin hanyoyin isa zuwa ga yardar Allah da samun kusanci zuwa gare shi.
Shahada ga al'umma ba asara bace, saboda gurin qoqarin kaiwa ne ga hadafi babba wanda Allah Ta'ala ke so ga mutum, wanda shine isa ga ɗa'ar shi, a yayin da mutum ke qoqarin sauke Taklifin ubangiji na tsare karamar al'umma da mutuncin musulmai da abubuwan da suke girmamawa. Imam Khumaini (Q.s) yana cewa,"Yana wajaba 'yan koren Amurka su sani cewa ita Shahada ba ya yiwuwa a kwatantata da galaba ko cin nasara a fagyagen yaqi, matsayin Shahada shine qarshe a bauta na yin sa'ayi da aiki a Duniyar nan ta Zahiri...", (Durus min kaɗɗil-Imamil-Khumainiy, 57).
Babu shakka cewa Lallai Shahada ni'ima ce babba ta ubangiji wacce yake bayarwa ga wanda ya so, a bayan shi kuma ya shirya mata,ba mutum ne zai qaddara wa kan shi ba.
Ai-imamul-Khumaniy (Q.s) yana cewa,"Lallai neman Shahada a gurinmu wani qari ne (Na falala) babba (A baya ga Tayuwa qyam har qarshen Rayuwa)". A wani gurin kuma yana cewa,"Ita Shahada wata kyauta ce daga Allah Tabaraka wa Ta'ala,ga wanda ya himmatu (Da aiki) Sai Allah ya ba shi ita", (Durus min kaɗɗil-Imamil-Khumainiy,57-58).
Zan ci gaba insha Allah
Comments
Post a Comment