YA ZA KA ZAMA SHAHIDI (II)
~Aɗɗalib Ahmad Harun
To ga wanda ke son wannan maqami sai ya himmatu da wa'innan siffofin dan ya zama ahlin Shahadar har Allah ya bashi:
1-Nisantar Duniya:Imma Duniyar nan na da qima to bai wuce dan kasancewarta hanyar isa zuwa ga neman yardar Allah ba.
A fahimtata abin da ake nufi da 'Zuhdu' gudun Duniya shine nisantar duk wani abu da zai nisantar da kai daga ubangijinka, koda ko jin daɗi ne. In ko na san cewa wannan jin daɗin zai nisanta ni da mahalicci na ta ya ba zan guje shi ba! Sannan da Kusantar duk wani abu da zai kusanta ni da mahalicci na,shima koda ko jin daɗin ne. Saboda kowane mutum shi ya san kanshi.
Tunda ko haka ne, ka ga ko bai kamata dan an ga wani ya nisan kayan aalaatun Duniya a matsayin Zuhudu sai ace ai wannan ba shi bane Gudun Duniya ba, la la la! Shi ya san kan shi. Allahumma sai dai in yana yi ne bisa rashin sani, sai a tunatar da shi abin da ya dace.
Rubutu zai zo na musamman dangane da Mafhumin Zuhudun insha Allah.
2-'Danfaruwa da makarantar Ashura:A makarantar Ashura mutum ke sanin abubuwan da addini ke koyar da tsayuwa da su, kamar sanin mutuntaka, Sadaukarwa, fifita wani akan kai, Miqa wiya, izza ga rai, da neman Tsayuwa qem a Rayuwa. Imam Khumaini (Q.s) na cewa a wannan gaɓar, "Mu bama damuwa idan aka zubar da jinanan matasanmu Tsarkaka a Tafarkin Musulunci, Ba mu damuwa idan Shahada ta zama abin gado ga maɗaukakanmu;Domin salo ne yardajje abin bi ga mabiya Amiril-mu'uminiin (A) Tun bayyanar Musulunci zuwa yau", (Durus min kaɗɗil-imamil-Khumainiy,59).
3-'Danfaruwa da Shahidai:Suma Shahidai dole a ɗanfaru da su, Ta hanyar karanta Tarihohinsu da wasiyyoyinsu, dan koyi da irin ayyukan sadaukarwar da su kai. Domin bibiyar abubuwan da suka shafi Shahidai yana motsa zukata da farkar da abubuwan da ke ɓoye (A zukatan) Wanda Shaiɗan ke qoqarin bebantar da su kuma ya shafe sautunsu wanda ke fuskantar gyara.
Lallai ɗanfaruwa da Shahidan na kusanta ruhin mutum da ruhikansu, har ya zama ɗaya daga cikin wa'inda suka shirya wa wannan Tagomashi na ubangiji wanda su (Shahidan) su ka haɗu da shi, wato Shahada.
Imam Khumaini ya sha qarfafawa a da yawa daga cikin Tarurruka cewa, lallai su Shahidai ana ɗaukarsu ne a jagororin Tafiya (Ta gwagwarmaya) Kuma lallai su ne masana a Duniyar Jahadi, ya kamata mu rinqa fa'idantuwa da su,(Durus min kaɗɗil-imamil-Khumainiy, 60).
4-Azama Tabbatatta da Himma Maɗaukakiya:Imam Khumaini (Q.s) na cewa,"Azama Tabbatatta da Himma Maɗaukakiya na Shahidai, suka Tabbatar da Dokokin Jamhuriyyar Musulunci a Iran, kuma Thauranmu ta zama cikin mafi ɗaukakar qololuwar izza da daraja wacce ta haska qofofi na shiriyar al'ummu masu qishin (Wannan shiriyar)",(Durus min kaɗɗil-imamil-Khumainiy, 61).
Mu haɗu a kashi na uku
Comments
Post a Comment