ZANGO NA ƘARSHE A TARON ƘARAWA JUNA SANI NA CIBIYAR WALLAFA

 Bayan shafe kwanaki biyu da shiga taron ƙarawa juna sani ga Marubutan Harka Muslunci wanda Cibiyar Wallafa Da Yaɗa Ayyukan Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ta shirya a garin Bauchi, yau Lahadi an shiga rana ta ƙarshe da za a rufe taron.
 Malam Ibrahim Aƙil shine Malami na farko da ya fara gabatar da jawabi a yau kan Maudu'i mai taken 'Tasirin Hoto Da Kimiyyar Dauƙarsa a bisa Ƙa'ida'. Malam Ibrahim Aƙil yayi jawabai sosai akan Maudu'in, inda a ƙarshe Muhammad Mukhtar Idris Kano ya gabatar da ta'aliƙi.

 Yanzu haka kuma babban baƙo mai rufe taron Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos shine yake kan gabatar da jawabi a muhallin bayan Malama Jamila Mukhtar Kaduna ta gabatar da Malam din. Ga mai buƙatan jawaban da ayi a wajen taron yana iya tuntubar mu.

 - Ibrahim Almustapha Saminaka
 - 4/Fubairu/2021

Comments

Popular posts from this blog

KAI TSAYE DAGA MINISTRY OF JUSTICE POTISKUM.

labari mai sosa Zuciya