003 WASIYYAR MANZON ALLAH (S) GA IMAM ALI (AS) GAME DA ZAMANTAKEWAR AURE KASHI NA (3).
TAREDA QA'EEM TV
*Manzon Allah (s) yace:*
*Ya Ali (as) kada mutum yasadu da iyalinsa a farkon wata (wato 1 ga wata) da tsakiyar wata(wato 15 ga wata)da karshan wata (wato 29 ko 30 ga wata).*
*Sai Manzon Allah(s) yace domin saduwa a* *wayannan lokuta guda uku yana gaggawan haifar da HAUKA DA KUTURTA ga ita matar da kuma dan da zata haifa.*
*Sai Manzon Allah(s) yakara cewa:*
*Ya Ali(as) kada mutum yasadu da iyalinsa bayan azuhur (wato bayan anyi sallar azuhur).*
*Domin idan Allah ya hukunta zaa samu karuwa ta haiuwa a wannan alokacin to dan za'a haifoshi sahuhu yana zubar da miyau abaki,shi kuma shaidan yana murna da irin wannan haihuwar.*
*Sai Manzon Allah(s) yace:*
*Ya Ali(as)kada mutum ya ringa yin magana alokacin da yake saduwa da iyalinsa.*
*Domin idan Allah ya hukunta zaa saamu karuwa ta da a wannan lokacin to lallai baa amintar da dan cewa zai iya zama baibai ba(wato yaron da aka Haifa zai iya zama wanda baya iya yin magana).*
*Insha Allah zamuci gaba.......*
*كتاب مكارم الاخلاق تأليف الشيخ الطبرسي (قدس)*
Comments
Post a Comment