004 WASIYYAR MANZON ALLAH (S) GA IMAM ALI (AS) GAME DA ZAMANTAKEWAR AURE KASHI NA (4)
TAREDA QA'EEM TV *Manzon Allah (s) yace:* *Ya Ali (s)Kada mutum ya ringa kallon al'auran matarshi a lokacin da yake saduwa da ita,ya kauda idonshi daga al'auranta,* *Domin kallon al'aurar yana haifar da makanta ga yaron da zasu haifa.* *Sai manzon Allah(s)yace:* *Ya Ali(as)Kada mutum yasadu da matarshi da sha'awar wata mace a tare dashi.* *Domin ina jima mutum tsoro idan aka kaddara samun karuwa ta da a wannan saduwa yazama dan an haifeshi mata maza kuma mahaukaci.* *sai manzon Allah(s)yace:* *Ya Ali(as)wanda yazama yanada janaba tare da matarshi akan shinfidarsu, to kada su karanta AQur'ani mai girma.* *Domin ina jimusu tsoro kada wuta ta sauka daga sama ta konasu (su maauratan).* *Zamuci gaba insha Allah........* *كتاب مكارم الاخلاق تأليف الشيخ الطبرسي (قدس)*