GOBE ZA A CIGABA DA HARAMTACCIYAR SHARI'AR DA AKE WA SHAIKH ZAKZAKY DA MATARSA A KADUNA Idan ba ku manta ba dama kotun ta dage cigaba da sauraron shaidun da Lauyoyin gwamnati suke gabatarwa ne zuwa ranar 8 da 9 ga watan Maris 2021. Tun a ranar Laraba da Alhamis 18-19/11/2020 ne Lauyoyin gwamnatin jihar Kaduna suka fara gabatar da shedunsu a kokarinsu na gamsar da kotu kan hauka da shirme da suke wa Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah, inda a ranar Laraba 18 ga Nuwambar suka gabatar da shedu biyu da suka hada da Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka, wanda yake tsohon kakakin rundunar sojan Nijeriya ne a lokacin kisan-kiyashin Zariya har zuwa ritayarsa. Ya tabbatar da cewa yana tare da tawagar Buratai a yayin kisan-kiyashin Zariya, sannan kuma bai yi magana da Shaikh Zakzaky ba a tsawon wannan lokacin. Shaidan lauyoyin gwamnati na biyu da suka gabatar shine Kanar Babayo Muhammad wanda, wanda yace a yanzu haka shine kwamandan 25 Birget a Damboa jihar Borno, kuma a lokacin da aka...