WASIYYAR MANZON ALLAH (S) GA IMAM ALI (AS) GAME DA ZAMANTAKEWAR AURE KASHI NA (2)
TAREDA QA'EEM TV *Manzon Allah (s) yace: Ya Ali (as) a satin farko na zuwan matarka gidanka ka hanata cin abubuwa guda hudu:* *1-Ka hanata shan Nono.* *2-Ka hanata shan abu mai tsami.* *3-Ka hanata cin kuzbarat (كزبرة) [wani ganye ne da ake sakawa acikin abinci yakan bada wani dandano a abinci.]* *4-Ka hanata cin Apple mai tsami.* *Sai Imam Ali (as)Yace:Ya manzon Allah(s) saboda me zan hana mata ta cin wadannan abubuwa guda hudu??* *sai manzon Allah (s) yace:Domin mahaifa tanayin sanyi kuma tana daina haihuwa saboda wayannan abubuwa guda hudu,kuma ka ajiye tabarma ajingine a jikin ginin gidanka it's tafi alkhairi akan matar da bata haihuwa.* *sai Imam Ali(as)yace:ya manzon Allah (s) meye matslar abu mai tsami da har zaa hana amarya daga gareshi???* *sai manzon Allah (s)yace:* *1-Idan mace tayi haila bayan tasha wannan abu mai tsami bazata kara samin cikakken tsarki na hailarta ba har abada.* *2-shi kuma ganyan kuzbarat (كزبرة) yana tayar da haila acikin mace, kum...